Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:137-146 Littafi Mai Tsarki (HAU)

137. Kai mai adalci ne, ya Ubangiji,Dokokinka kuma daidai ne,

138. Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne,Daidai ne kuwa.

139. Fushi yana cina kamar wuta,Saboda maƙiyana ba su kula da umarnanka ba.

140. Alkawarinka ba ya tashi!Bawanka yana ƙaunar alkawarinka ƙwarai!

141. Ni ba kome ba ne, rainanne ne,Amma ban ƙi kula da ka'idodinka ba.

142. Adalcinka zai tabbata har abada,Dokarka gaskiya ce koyaushe.

143. A cike nake da wahala da damuwa,Amma umarnanka suna faranta zuciyata.

144. Koyarwarka masu adalci ne har abada,Ka ba ni ganewa domin in rayu.

145. Ina kira gare ka da zuciya ɗaya,Ka amsa mini, ya Ubangiji,Zan yi biyayya da umarnanka!

146. Ina kira gare ka,Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!

Karanta cikakken babi Zab 119