Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Zan ta da murya,In maimaita dukan dokokin da ka bayar.

14. Ina murna da bin umarnanka,Fiye da samun dukiya mai yawa.

15. Nakan yi nazarin umarnanka,Nakan kuma yi bimbinin koyarwarka.

16. Ina murna da dokokinka,Ba zan manta da umarnanka ba.

17. Ka yi mini alheri, ni bawanka,Domin in rayu in yi biyayya da koyarwarka.

18. Ka buɗe idonaDomin in ga gaskiyar shari'arka mai banmamaki.

19. Zamana a nan duniya na ɗan lokaci kaɗan ne.Kada ka ɓoye mini umarnanka!

20. Zuciyata ta ƙosa saboda marmari,A kowane lokaci ina so in san hukuntanka.

21. Kakan tsauta wa masu girmankai,La'anannu ne waɗanda suka ƙi bin umarnanka.

22. Ka kuɓutar da ni daga cin mutuncinsu da raininsu,Domin na kiyaye dokokinka.

Karanta cikakken babi Zab 119