Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:127-138 Littafi Mai Tsarki (HAU)

127. Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya,Fiye da zinariya tsantsa.

128. Saboda haka ina bin dukan koyarwarka,Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.

129. Koyarwarka tana da ban al'ajabi,Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.

130. Fassarar koyarwarka takan ba da haske,Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.

131. Ina haki da baki a buɗe,Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.

132. Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai,Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.

133. Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta,Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.

134. Ka cece ni daga waɗanda suke zaluntata,Domin in yi biyayya da umarnanka.

135. Ka sa mini albarka da kasancewarka tare da ni,Ka koya mini dokokinka.

136. Hawayena suna malalowa kamar kogi,Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.

137. Kai mai adalci ne, ya Ubangiji,Dokokinka kuma daidai ne,

138. Ka'idodin da ka bayar kuwa dukansu masu kyau ne,Daidai ne kuwa.

Karanta cikakken babi Zab 119