Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:124-133 Littafi Mai Tsarki (HAU)

124. Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka,Ka koya mini umarnanka.

125. Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa,Don in san koyarwarka.

126. Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu,Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!

127. Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya,Fiye da zinariya tsantsa.

128. Saboda haka ina bin dukan koyarwarka,Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.

129. Koyarwarka tana da ban al'ajabi,Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.

130. Fassarar koyarwarka takan ba da haske,Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.

131. Ina haki da baki a buɗe,Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.

132. Ka juyo wurina ka yi mini jinƙai,Kamar yadda kakan yi wa masu ƙaunarka.

133. Kada ka bar ni in fāɗi kamar yadda ka alkawarta,Kada ka bar mugunta ta rinjaye ni.

Karanta cikakken babi Zab 119