Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:119-131 Littafi Mai Tsarki (HAU)

119. Kakan yi banza da duk mai mugunta,Don haka ina ƙaunar koyarwarka.

120. Saboda kai, nake jin tsoro,Na cika da tsoro saboda shari'unka.

121. Na yi abin da yake daidai mai kyau,Kada ka bar ni a hannun maƙiyana!

122. Sai ka yi alkawari za ka taimaki bawanka,Kada ka bar masu girmankai su wahalshe ni!

123. Idanuna sun gaji da duban hanyar cetonka,Ceton da ka alkawarta.

124. Ka bi da ni bisa ga tabbatacciyar ƙaunarka,Ka koya mini umarnanka.

125. Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa,Don in san koyarwarka.

126. Ya Ubangiji, lokaci ya yi da za ka yi wani abu,Saboda mutane sun ƙi yin biyayya da dokarka!

127. Ina ƙaunar umarnanka, fiye da zinariya,Fiye da zinariya tsantsa.

128. Saboda haka ina bin dukan koyarwarka,Ina kuwa ƙin dukan mugayen al'amura.

129. Koyarwarka tana da ban al'ajabi,Da zuciya ɗaya nake biyayya da su.

130. Fassarar koyarwarka takan ba da haske,Takan ba da hikima ga wanda bai ƙware ba.

131. Ina haki da baki a buɗe,Saboda marmarin da nake yi wa umarnanka.

Karanta cikakken babi Zab 119