Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 119:108-121 Littafi Mai Tsarki (HAU)

108. Ka karɓi addu'ata ta godiya, ya Ubangiji,Ka koya mini umarnanka.

109. Kullum a shirye nake in kasai da raina,Ban manta da umarninka ba.

110. Mugaye sun kafa mini tarko,Amma ban yi rashin biyayya da umarnanka ba.

111. Umarnanka nawa ne har abada, Su ne murnar zuciyata.

112. Na ƙudura zan yi biyayya da ka'idodinka,Har ranar mutuwata.

113. Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci,Amma ina ƙaunar dokarka.

114. Kai ne kake kāre ni, kake kuma kiyaye ni,Ina sa zuciya ga alkawarinka.

115. Ku rabu da ni, ku masu zunubi!Zan yi biyayya da umarnan Allahna.

116. Ka ƙarfafa ni kamar yadda ka alkawarta, zan kuwa rayu,Kada ka bar ni in kasa ci wa burina!

117. Ka riƙe ni, sai in zauna lafiya,Koyaushe zan mai da hankali ga umarnanka.

118. Ka rabu da dukan waɗanda ba su biyayya da dokokinka,Dabarunsu na yaudara banza ne.

119. Kakan yi banza da duk mai mugunta,Don haka ina ƙaunar koyarwarka.

120. Saboda kai, nake jin tsoro,Na cika da tsoro saboda shari'unka.

121. Na yi abin da yake daidai mai kyau,Kada ka bar ni a hannun maƙiyana!

Karanta cikakken babi Zab 119