Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 114:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Duwatsu suka yi ta tsalle kamar awaki,Tuddai kuwa suka yi ta tsalle suna kewayawa kamar tumaki.

5. Me ya faru ne, ya teku, da ya sa ki gudu?Kai fa Urdun, me ya sa ka daina gudu?

6. Ku fa duwatsu, me ya sa kuka yi ta tsalle kamar awaki?Tuddai, me ya sa kuka yi ta tsalle,Kuna kewayawa kamar tumaki?

7. Ki yi rawar jiki, ya ke duniya,Saboda zuwan Ubangiji,A gaban Allah na Yakubu,

8. Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa,Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai,Masu bulbulo da ruwa.

Karanta cikakken babi Zab 114