Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 114:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da jama'ar Isra'ila suka bar Masar,Sa'ad da zuriyar Yakubu suka bar baƙuwar ƙasar nan,

2. Yahuza ya zama tsattsarkar jama'ar Ubangiji,Isra'ila ya zama abin mallakarsa.

3. Bahar Maliya da ya duba, sai ya gudu,Kogin Urdun ya daina gudu.

4. Duwatsu suka yi ta tsalle kamar awaki,Tuddai kuwa suka yi ta tsalle suna kewayawa kamar tumaki.

Karanta cikakken babi Zab 114