Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 110:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina,“Zauna nan a damana,Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”

2. Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce,“Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”

3. A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka,Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu.Kamar yadda raɓa take da sassafe,Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.

4. Ubangiji ya yi muhimmin alkawari,Ba kuwa zai fasa ba!“Za ka zama firist har abadaBisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.”

5. Ubangiji yana damanka,Zai kori sarakuna a ranar da ya husata.

6. Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma,Ya rufe fagen fama da gawawwaki,Zai kori sarakunan duk duniya.

7. Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya,Ya wartsake ya sami ƙarfi.Zai yi tsayawar nasara.

Karanta cikakken babi Zab 110