Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 109:20-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Ya Ubangiji, ka sa haka,Wato ya zama yadda za a hukunta wa maƙiyana ke nan,Waɗanda suke faɗar mugayen abubuwa a kaina!

21. Amma ya Ubangiji, Allahna, ka taimake ni,Yadda ka alkawarta,Ka cece ni sabili da alherin ƙaunarka.

22. Ni talaka ne, matalauci,Na ji zafi ƙwarai a can zuciyata.

23. Na kusa ɓacewa kamar inuwar maraice,An hurar da ni can kamar ƙwaro.

24. Gwiwoyina sun yi suwu saboda rashin abinci,Jikina kuma ya rame, ba shi da ƙarfi.

25. Sa'ad da mutane suka gan ni sun yi mini ba'a,Suna kaɗa kai saboda raini.

26. Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna,Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!

27. Ka sa maƙiyana su sani,Kai ne Mai Cetona.

28. Watakila su la'anta ni,Amma kai za ka sa mini albarka,Ka sa a kori waɗanda suke tsananta mini.Da ma ka sa ni da nake bawanka, in yi murna.

29. Ka sa kunya ta rufe maƙiyana,Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.

30. Da murya mai ƙarfi zan yi wa Ubangiji godiya.Zan yabe shi a taron jama'a,

31. Saboda yakan kāre talaka,Domin ya cece shi daga waɗandaSuka sa masa laifin mutuwa.

Karanta cikakken babi Zab 109