Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 108:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Zan yi maka godiya a tsakiyar sauran al'umma, ya Ubangiji!Zan yabe ka a tsakiyar kabilai!

4. Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har can saman sammai,Amincinka kuma ya kai sararin sammai.

5. Ya Allah, ka bayyana girmanka a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!

6. Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.

7. A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,“Da nasara zan raba Shekem,Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.

8. Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,Ifraimu ne kwalkwalina,Yahuza kuma sandana ne na sarauta.

9. Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki,Edom kuwa kamar akwatin takalmina.Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”

Karanta cikakken babi Zab 108