Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 107:32-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Dole su yi shelar girmansa cikin taron jama'a,Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.

33. Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf,Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.

34. Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani,Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.

35. Ya sāke hamada ta zama tafkunan ruwa,Ya kuma mai da busasshiyar ƙasa ta zama maɓuɓɓugai masu gudana.

36. Ya bar mayunwata su zauna a can,Suka kuwa gina birni don su zauna a ciki.

37. Suka shuka gonaki suka dasa kurangar inabi,Waɗanda suka ba da amfani mai yawan gaske.

38. Ya sa wa jama'arsa albarka,Suka kuwa haifi 'ya'ya da yawa.Bai bar garkunan shanunsu su ragu ba.

39. Sa'ad da aka ci nasara a kan jama'ar Allah,Aka ƙasƙantar da su ta wurin mugun zalunci,Da wahalar da aka yi musu.

40. Sai Allah ya wulakanta waɗanda suka zalunci jama'arsa.Ya sa su suka yi ta kai da kawowaA hamada inda ba hanya.

41. Ya tsamo masu bukata daga cikin baƙin cikinsu,Ya sa iyalansu su riɓaɓɓanya kamar garkunan tumaki.

42. Da adalai suka ga wannan, sai suka yi murna,Mugaye kuwa aka rufe bakinsu.

43. Da ma a ce masu hikimaZa su yi tunani a kan waɗannan abubuwa,Da ma kuma su yardaDa madawwamiyar ƙaunar Ubangiji.

Karanta cikakken babi Zab 107