Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 107:3-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ya komo da ku daga ƙasashen waje,Daga gabas da yamma, kudu da arewa.

4. Waɗansu suka yi ta kai da kawowa a hamada inda ba hanya,Sun kasa samun hanyar da za ta kai su garin da za su zauna a ciki.

5. Suka yi ta fama da yunwa, da ƙishirwa,Suka fid da zuciya ga kome.

6. Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga wahalarsu.

7. Ya fisshe su, ya bi da su sosai,Zuwa birnin da za su zauna.

8. Dole ne su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu!

9. Ya shayar da waɗanda suke jin ƙishirwa,Ya kuma ƙosar da mayunwata da alheransa.

10. Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa,'Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,

11. Saboda sun tayar, sun ƙi bin umarnan Allah Maɗaukaki,Sun kuwa ƙi koyarwarsa.

12. Suka gaji tiƙis saboda tsananin aiki,Za su faɗi ƙasa, ba mataimaki.

13. A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga wahalarsu.

14. Ya fisshe su daga cikin duhu da inuwar mutuwa,Ya tsintsinka sarƙoƙinsu.

Karanta cikakken babi Zab 107