Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 107:25-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi,Ta fara hurowa, ta sa raƙuman ruwa su tashi.

26. Aka ɗaga jiragen ruwa sama,Sa'an nan suka tsinduma cikin zurfafa.Da mutanen suka ga irin hatsarin da suke ciki,Sai zuciyarsu ta karai.

27. Suka yi ta tuntuɓe suna ta tangaɗi kamar bugaggu,Gwanintarsu duka ta zama ta banza.

28. Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga azabarsu.

29. Ya sa hadiri ya yi tsit,Raƙuman ruwa kuma suka yi shiru.

30. Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru,Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya,Wurin da suke so.

31. Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.

32. Dole su yi shelar girmansa cikin taron jama'a,Su kuma yabe shi a gaban majalisar dattawa.

33. Ubangiji ya sa koguna suka ƙafe ƙaƙaf,Ya hana maɓuɓɓugai su gudana.

34. Ya mai da ƙasa mai dausayi ta zama mai gishiri, marar amfani,Saboda muguntar waɗanda suke zaune a can.

Karanta cikakken babi Zab 107