Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 106:33-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Suka sa Musa ya husata ƙwarai,Har ya faɗi abubuwan da bai kamata ya faɗa ba.

34. Suka ƙi su kashe arna,Yadda Ubangiji ya umarta,

35. Amma suka yi aurayya da su,Suka kwaikwayi halayen arnan.

36. Jama'ar Allah suka yi wa gumaka sujada.Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.

37. Suka miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga allolin arna.

38. Suka karkashe mutane marasa laifi,Wato 'ya'yansu mata da maza.Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana,Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.

39. Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu,Suka zama marasa aminci ga Allah.

Karanta cikakken babi Zab 106