Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 106:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ya cece su daga maƙiyansu,Ya ƙwato su daga wurin abokan gābansu.

11. Ruwa ya cinye maƙiyansu,Ba wanda ya tsira.

12. Sa'an nan jama'arsa suka gaskata alkawarinsa,Suka raira yabo gare shi.

13. Amma nan da nan, suka manta da abin da ya yi,Suka aikata, ba su jira shawararsa ba.

14. Suka cika da sha'awa cikin hamada,Suka jarraba Allah,

15. Sai ya ba su abin da suka roƙa,Amma ya aukar musu da muguwar cuta.

16. Can cikin hamada suka ji kishin MusaDa Haruna, bayin Ubangiji, tsarkaka,

17. Sai ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan,Ta binne Abiram da iyalinsa.

18. Wuta ta sauko bisa magoya bayansu,Ta ƙone mugayen mutanen nan.

19. Suka ƙera ɗan maraƙi da zinariya a Horeb,Suka yi masa sujada.

Karanta cikakken babi Zab 106