Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 105:40-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

40. Suka roƙa, sai aka ba su makware,Ya ba su abinci daga sama da za su ci su ƙoshi.

41. Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo,Yana gudu cikin hamada kamar kogi.

42. Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkiWanda ya yi wa bawansa Ibrahim.

43. Haka kuwa ya bi da jama'arsa, suka fita suna raira waƙa,Ya bi da zaɓaɓɓun jama'arsa, suna sowa ta farin ciki.

44. Ya ba su ƙasar baƙi,Ya sa su gāje gonakinsu,

45. Don jama'arsa su yi biyayya da dokokinsa,Su kuma kiyaye umarninsa.Ku yabi Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 105