Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 105:25-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ya sa Masarawa suka ƙi jinin jama'arsa,Suka yi wa bayinsa munafunci.

26. Sai ya aiki bayinsa Musa da Haruna, waɗanda ya zaɓa.

27. Suka aikata manya manyan ayyuka na Allah,Suka kuma yi ayyukan al'ajabi a Masar.

28. Ya aika da duhu a bisa ƙasar.Musa da Haruna ba su tayar wa umarnansa ba.

29. Ya mai da ruwan kogunansu su zama jini,Ya karkashe kifayensu duka.

30. Ƙasarsu ta cika da kwaɗi,Har a fādar sarki.

31. Allah ya ba da umarni, sai ƙudaje da ƙwariSuka cika dukan ƙasar.

32. Ya aiki ƙanƙara da tsawa a bisa ƙasarsuMaimakon ruwan sama.

Karanta cikakken babi Zab 105