Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 104:5-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ka sa duniya ta kahu sosai a bisa harsashin gininta,Ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.

6. Ka sa teku a bisanta kamar alkyabba,Ruwan kuwa ya rufe manyan duwatsu.

7. Amma sa'ad da ka tsauta wa ruwa,Sai ya tsere,Sa'ad da ya ji ka daka tsawa,Sai ya sheƙa a guje.

8. Ya haura kan duwatsu, ya gangara cikin kwaruruka,Wurin da ka shirya masa.

9. Ka ƙayyade masa kan iyaka da ba zai taɓa ƙetarewa ba,Don kada ya sāke rufe duniya.

10. Ka sa maɓuɓɓugai suka gudano cikin kwaruruka,Ka sa ruwa yana gudu tsakanin tuddai.

11. Su ne suke shayar da namomin jeji,Jakunan jeji kuma, a nan sukan kashe ƙishinsu.

12. A itatuwan da suke kusa da wurin,Tsuntsaye suke yin sheƙunansu suna ta raira waƙa.

13. Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu,Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.

14. Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu,Tsire-tsire kuma don amfanin mutum,Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,

15. Don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki,Ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara'a,Da abincin da zai ba shi ƙarfi.

Karanta cikakken babi Zab 104