Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 104:10-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ka sa maɓuɓɓugai suka gudano cikin kwaruruka,Ka sa ruwa yana gudu tsakanin tuddai.

11. Su ne suke shayar da namomin jeji,Jakunan jeji kuma, a nan sukan kashe ƙishinsu.

12. A itatuwan da suke kusa da wurin,Tsuntsaye suke yin sheƙunansu suna ta raira waƙa.

13. Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu,Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.

14. Kakan sa ciyawa ta yi girma don shanu,Tsire-tsire kuma don amfanin mutum,Saboda haka mutum zai iya shuka amfanin gona,

15. Don ya yi ruwan inabin da zai sa shi farin ciki,Ya sami man zaitun wanda zai sa shi fara'a,Da abincin da zai ba shi ƙarfi.

16. Itatuwan al'ul na Lebanon sukan sami isasshen ruwan sama,Itatuwa ne na Ubangiji kansa, waɗanda shi ya dasa.

17. A nan tsuntsaye suke yin sheƙunansu,A bisa itatuwan fir shamuwa suke yin sheƙa.

18. A kan duwatsu masu tsayi awakin jeji suke zama,Remaye sukan ɓuya a kan tsaunukan bakin teku.

19. Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai,Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.

20. Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.

21. Sagarun zakoki sukan yi ruri sa'ad da suke farauta,Suna neman abincin da Allah zai ba su.

22. Sa'ad da rana ta fito,Sai su koma su kwanta a kogwanninsu.

23. Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu,Su yi ta aiki har maraice ya yi.

24. Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa!Da hikima ƙwarai ka halicce su!Duniya cike take da talikanka.

25. Ga babbar teku mai fāɗi,Inda talikai da ba su ƙidayuwa suke zaune,Manya da ƙanana gaba ɗaya.

26. Jiragen ruwa suna tafiya a kansa,Dodon ruwa wanda ka halitta, a ciki yake wasa.

27. Dukansu a gare ka suke dogara,Don ka ba su abinci sa'ad da suke bukata.

Karanta cikakken babi Zab 104