Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 101:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ba zan yi rashin aminci ba,Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.

5. Zan hallakar da mai raɗar abokinsa,Ba zan jure da mutum mai girmankai,Ko mai alfarma ba.

6. Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah,Zan yardar musu si yi zamansu a fādata,Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminciSu yi mini hidima.

7. Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba,Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba.

8. A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu,Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji.

Karanta cikakken babi Zab 101