Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 9:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ubangiji ya ce, “Kowace irin muguntarsu tana a Gilgal,A can na ƙi su!Saboda mugayen ayyukansu, zan kore su daga ƙasata,Ba kuma zan ƙaunace su ba.Dukan shugabanninsu 'yan tayarwa ne.

16. An ka da mutanen Ifraimu, saiwarsu ta bushe.Ba za su yi 'ya'ya ba.Ko ma sun haihu, zan kashe 'ya'yan nan nasu waɗanda suke ƙauna.”

17. Allahna zai ƙi suDomin ba su yi masa biyayya ba.Za su zama masu yawo cikin al'ummai.

Karanta cikakken babi Yush 9