Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 8:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki,Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji,Domin mutanena sun ta da alkawarina,Sun kuma keta dokokina.

2. Sun yi kuka a wurina,Suna cewa, ‘Ya Allah, mu Isra'ila mun san ka!’

3. Isra'ila ta ƙi abin da yake mai kyau,Don haka abokan gāba sun fafare ta.

4. “Suna naɗa sarakuna, amma ba da iznina ba.Suna naɗa shugabanni amma ba da yardata ba.Suna ƙera gumaka da azurfarsu da zinariyarsu,Wannan kuwa zai zama sanadin halakarsu.

5. Ya mutanen Samariya, ina ƙin maraƙinku na siffa.Ina jin haushinsu ƙwarai!Sai yaushe za su rabu da gumaka?

6. Ai, mai aikin hannu ne ya yi shi a Isra'ila!Gunki ne ba Allah ba ne.Za a farfashe siffar maraƙin Samariya.

7. Gama sun shuka iskaDon haka zu su girbe guguwa.Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya,Ba zai yi tsaba ba.Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,

8. Isra'ila kamar kowace al'umma ce.Suna cikin al'ummaiKamar kaskon da ba shi da amfani,

9. Gama sun haura zuwa Assuriya,Kamar jakin jeji da yake yawo shi kaɗai.Mutanen Ifraimu sun yi ijara da abokan tsafinsu.

10. Ko da yake sun yi ijara da abokai daga cikin al'ummai,Yanzu zan tattara su, in hukunta su.Sa'an nan za su fara ragowa,Ta wurin tunanin nawayar Sarkin sarakuna.

Karanta cikakken babi Yush 8