Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

An Tsauta wa Isra'ila domin Tsafi

1. Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki,Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji,Domin mutanena sun ta da alkawarina,Sun kuma keta dokokina.

2. Sun yi kuka a wurina,Suna cewa, ‘Ya Allah, mu Isra'ila mun san ka!’

3. Isra'ila ta ƙi abin da yake mai kyau,Don haka abokan gāba sun fafare ta.

4. “Suna naɗa sarakuna, amma ba da iznina ba.Suna naɗa shugabanni amma ba da yardata ba.Suna ƙera gumaka da azurfarsu da zinariyarsu,Wannan kuwa zai zama sanadin halakarsu.

5. Ya mutanen Samariya, ina ƙin maraƙinku na siffa.Ina jin haushinsu ƙwarai!Sai yaushe za su rabu da gumaka?

6. Ai, mai aikin hannu ne ya yi shi a Isra'ila!Gunki ne ba Allah ba ne.Za a farfashe siffar maraƙin Samariya.

7. Gama sun shuka iskaDon haka zu su girbe guguwa.Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya,Ba zai yi tsaba ba.Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,

8. Isra'ila kamar kowace al'umma ce.Suna cikin al'ummaiKamar kaskon da ba shi da amfani,

9. Gama sun haura zuwa Assuriya,Kamar jakin jeji da yake yawo shi kaɗai.Mutanen Ifraimu sun yi ijara da abokan tsafinsu.

10. Ko da yake sun yi ijara da abokai daga cikin al'ummai,Yanzu zan tattara su, in hukunta su.Sa'an nan za su fara ragowa,Ta wurin tunanin nawayar Sarkin sarakuna.

11. “Da yake Ilfraimu ta yawaita bagadan zunubi,Sun zama mata bagadai na yin zunubi.

12. Ko da na rubuta mata dokokina sau da yawo,Za ta ɗauke su wani baƙon abu ne kawai.

13. Suna jin daɗin miƙa hadayu don cin naman,Amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu.Ubangiji zai tuna da muguntarsu,Zai hukunta su saboda zunubansu.Za su koma Masar.

14. “Gama mutanen Isra'ila sun manta da Mahaliccinsu,Sai sun gina manyan gidaje masu daraja.Mutanen Yahuza kuma sun yawaita biranensu masu garu,Amma ni Ubangiji, zan aika da wuta a kan biranensu,Ta ƙone fādodinsu.”