Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 7:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Sa'ad da zan warkar da mutanen Isra'ila,Sai zunubin Ifraimu da muguntar Samariya su bayyana,Gama suna cin amana.Ɓarawo yakan fasa, ya shiga,'Yan fashi suna fashi a fili,

2. Amma ba su tunani,Cewa zan tuna da dukan muguntarsu.Yanzu ayyukansu sun kewaye su,Ina ganinsu.

3. “Suna faranta zuciyar sarki da muguntarsu,Na shugabanni kuma da ƙarairayinsu.

4. Dukansu mazinata ne,Suna kama da tanda da aka zafafa,Wadda matoyi ya daina iza mata wuta,Tun daga lokacin cuɗe kulluHar zuwa lokacin da yisti ya tasar da shi.

5. A ranar bikin sarki,Sukan sa sarki da shugabanni su bugu da ruwan inabi.Yakan yi cuɗanya da shakiyai.

6. Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu.Fushinsu na ci dare farai,Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.

7. “Dukansu suna da zafi kamar tanderu.Suna kashe masu mulkinsu.Dukan sarakunansu sun faɗi.Ba wanda ya kawo mini kuka.”

8. Ubangiji ya ce, “Mutanen Ifraimu sun haɗa kansu da al'ummai,Sun zama kamar wainar da ba a juya ba.

9. Baƙi sun cinye ƙarfinsu, su kuwa ba su sani ba,Furfura ta faso musu, amma ba su sani ba.

Karanta cikakken babi Yush 7