Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 6:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu,Na karkashe su da maganar bakina.Hukuntaina suna kama da hasken da yake ketowa.

6. Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba,Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.

7. “Amma sun ta da alkawarina kamar Adamu,Sun ci amanata.

8. Gileyad gari ne na masu aikata mugunta.Tana da tabban jini.

9. Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum,Haka nan firistoci suka haɗa kansuDon su yi kisankai a hanyar Shekem,Ai, sun aikata mugayen abubuwa.

10. Na ga abin banƙyama a cikin Isra'ila,Karuwancin Ifraimu yana wurin,Isra'ila ta ƙazantar da kanta.

11. “Ku kuma, ya mutanen Yahuza, an shirya muku ranar girbi,A lokacin da zan mayar wa mutanena da dukiyarsu.”

Karanta cikakken babi Yush 6