Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 5:9-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ifraimu za ta zama kango a ranar hukunci.A kabilan Isra'ila na sanar da abin da zai faru, ba makawa.

10. “Shugabannin Yahuza sun zama kamar masu cin iyaka,Zan zubo musu da fushina kamar ruwa.

11. An danne Ifraimu, shari'a ta murƙushe ta,Domin ta ƙudura ta bi banza.

12. Domin haka na zama kamar asu ga Ifraimu,Kamar ruɓa ga mutanen Yahuza.

13. “Sa'ad da Ifraimu ta ga ciwonta,Yahuza kuma ta ga rauninta,Sai Ifraimu ta aika zuwa Assuriya,Wurin babban sarki.Amman ba zai iya warkar da ciwonki, ko rauninki ba.

14. Zan zama kamar zaki ga Ifraimu,Kamar sagarin zaki ga mutanen Yahuza.Ni kaina zan yayyage, in yi tafiyata.Zan ɗauka, in tafi, ba wanda zai yi ceto.

Karanta cikakken babi Yush 5