Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 2:16-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ni Ubangiji na ce, a waccan ranaZa ta ce da ni,‘Mijina,’ ba za ta ƙara ce da ni Ba'al ba.

17. Zan kawar da sunayen Ba'al daga bakinta.Ba za a ƙara kiransu da sunayensu ba.

18. “A waccan rana zan yi alkawariDa namomin jeji, da tsuntsaye,Da abubuwa masu rarrafe saboda Isra'ila.Zan kuma kakkarya baka da takobi,In kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar,Sa'an nan za su yi zamansu lami lafiya.

19. Zan ɗaura auren da yake cikin adalci,Da bisa kan ka'ida, da ƙauna.

20. Zan ɗaura auren da yake cikin aminci,Za ki kuwa sani, ni ne Ubangiji.

21. “A waccan rana, zan amsa wa sammai,Su kuma za su amsa wa ƙasa.

22. Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, da ruwan inabi, da mai,Su ma za su amsa wa Yezreyel.

23. Zan dasa ta a ƙasa domin kaina.Zan kuma yi wa ‘Ba-jinƙai,’ jinƙai,In kuma ce wa ‘Ba-mutanena ba,’ ‘Mutanena!’Su ma za su ce, ‘Kai ne Allahna!’ ”

Karanta cikakken babi Yush 2