Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 2:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ka ce wa 'yan'uwanka maza, ‘Ku mutanena ne,’ ka kuma ce wa 'yar'uwarka, ‘Kin sami jinƙai!’

2. Ku roƙi uwarku,Gama ita ba matata ba ce,Ni kuma ba mijinta ba ne.Ku roƙe ta ta daina karuwancinta,Ta rabu da masu rungumar mamanta.

3. In ba haka ba, sai in yi mata tsiraici,In bar ta kamar ran da aka haife ta.In maishe ta kamar jeji,In bar ta kamar busasshiyar ƙasa,In kashe ta da ƙishi.

4. Ba zan yi wa 'ya'yanta jinƙai ba,Domin su 'ya'yan karuwanci ne

5. Gama uwarsu ta yi karuwanci.Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya.Gama ta ce, ‘Zan bi samarinaWaɗanda suke ba ni ci da sha,Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.’

6. “Don haka zan shinge hanyarta da ƙaya,Zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita.

7. Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba.Za ta neme su, amma ba za ta same su ba.Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari,Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’

8. “Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai,Da azurfa, da zinariya da yawaWaɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.

9. Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa,Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilinWaɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.

10. Yanzu zan buɗe tsiraicintaA idon samarinta,Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.

11. Zan sa ta daina farin cikinta,Da idodinta, da kiyaye lokatan amaryar wata,Da hutawar ranar Asabar,Da ƙayyadaddun idodinta.

12. Zan ɓata inabinta da itatuwan ɓaureWaɗanda take cewa, ‘Waɗannan su ne hakkinaWanda samarina suka ba ni.’Zan sa su zama kurmi,Namomin jeji su cinye su.

Karanta cikakken babi Yush 2