Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 11:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Mutanena sun himmantu su rabu da ni,Ko da yake an kira su ga Ubangiji,Ba wanda ya girmama shi.

8. “Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu?Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila?Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma?Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim?Zuciyata tana motsawa a cikina,Juyayina ya huru.

9. Ba zan aikata fushina mai zafi ba,Ba zan ƙara hallaka Ifraimu ba,Gama ni Allah ne, ba mutum ba,Maitsarki wanda yake tsakiyarku,Ba zan zo wurinku da hasala ba.

10. “Za su bi Ubangiji,Zai yi ruri kamar zaki, hakika zai yi ruri'Ya'yansa za su zo da rawar jiki da yamma.

11. Da sauri za su zo kamar tsuntsaye daga Masar,Kamar kurciyoyi daga ƙasar Assuriya,Zan komar da su gidajensu, ni Ubangiji na faɗa.”

12. Ubangiji ya ce, “Ifraimu ta kewaye ni da ƙarairayi,Jama'ar Isra'ila kuwa ta kewaye ni da munafuncinta,Yahuza kuma ta tayar wa Allah,Wato tana gāba da Mai Tsarki, mai aminci.

Karanta cikakken babi Yush 11