Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 11:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “A lokacin da Isra'ila yake yaro, na ƙaunace shi,Daga cikin Masar na kirawo ɗana.

2. Yawan kiransu, yawan tayarwar da suke yi mini,Sai ƙara miƙa wa Ba'al sadaka suke yi,Suna ƙona turare ga gumaka.

3. Ko da yake ni ne na koya wa Ifraimu tafiya.Na ɗauke su a hannuna,Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.

4. Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna,Na zama musu kamar wanda yake ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu.Na sunkuya, na ciyar da su.

5. “Ba su koma ƙasar Masar ba,Amma Assuriya za ta zama sarkinsuGama sun ƙi yarda su koma wurina.

6. Takobi zai ragargaje biranensu,Zai lalatar da sandunan ƙarafan ƙofofinsu,Zai cinye su domin muguwar shawararsu.

Karanta cikakken babi Yush 11