Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 4:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Amma kashegari da fitowar rana, sai Allah ya sa tsutsa ta cinye 'yar kurangar har ta mutu.

8. A sa'ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro. Yunusa ya ji kamar zai suma saboda zafin rana da take bugun kansa. Sai ya so ya mutu, ya ce, “Gara in mutu da ina zaune da rai.”

9. Amma Allah ya ce masa, “Daidai ne ka yi fushi saboda 'yar kurangar?”Yunusa ya amsa, “Hakika, daidai ne a gare ni in yi fushi, har ma in yi fushin da ya isa in mutu!”

10. Ubangiji kuma ya amsa, ya ce masa, “Ai, wannan 'yar kurangar dare ɗaya ta girma, kashegari kuma ta mutu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓaci saboda ita!

11. Ashe, dole ne ni kuma in ji tausayin Nineba, babban birni mai 'yan yara fiye da dubu ɗari da dubu ashirin marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa.”

Karanta cikakken babi Yun 4