Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 2:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Na ce, an kore ni daga wurinka,Duk da haka zan sāke ganinHaikalinka mai tsarki.

5. Ruwa ya sha kaina,Tekun ta rufe ni ɗungum.Tsire-tsiren teku suka naɗe kaina.

6. Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussanduwatsu.Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada,Amma ka fitar da ni daga cikinramin, ya Ubangiji Allahna.

7. Sa'ad da na ji raina yana rabuwa dani,Sai na tuna da kai, ya Ubangiji.Addu'ata kuwa ta kai gare ka aHaikalinka tsattsarka.

8. Su waɗanda suke yin sujada ga gumakamarasa amfaniSun daina yi maka biyayya.

9. Amma ni zan raira yabbai gare ka,Zan miƙa maka sadaka,Zan cika wa'adin da na yi.Ceto daga wurin Ubangiji yake.”

Karanta cikakken babi Yun 2