Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 2:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Yunusa ya yi addu'a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin,

2. ya ce,“A cikin wahalata na yi kira gare ka,ya Ubangiji,Ka a kuwa amsa mini.Daga can cikin lahira na yi kira,Ka kuwa ji muryata.

3. Ka jefa ni cikin zurfi,Can cikin tsakiyar teku,Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni,Kumfa da raƙuman ruwanka sukabi ta kaina.

4. Na ce, an kore ni daga wurinka,Duk da haka zan sāke ganinHaikalinka mai tsarki.

5. Ruwa ya sha kaina,Tekun ta rufe ni ɗungum.Tsire-tsiren teku suka naɗe kaina.

Karanta cikakken babi Yun 2