Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 1:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Dukan matuƙan jirgin suka firgita, sai kowannensu ya shiga roƙon allahnsa. Suka yi ta jefar da kayan da suke cikin jirgin a ruwa don su sami sauƙi. Yunusa kuwa yana can cikin jirgi, a kwance, yana ta sharar barci.

6. Can shugaban jirgin ya iske shi, ya ce masa, “Me ya sa kake barci? Tashi ka roƙi allahnka, watakila allahnka zai ji tausayinmu, yă cece mu.”

7. Matuƙan jirgin kuwa suka ce wa junansu, “To, bari mu jefa kuri'a mu gani ko alhakin wane ne ya jawo mana wannan bala'i da muke ciki.” Sai suka jefa kuri'a, kuri'ar kuwa ta fāɗa a kan Yunusa.

8. Suka ce masa, “Ka faɗa mana, laifin wane ne ya jawo mana wannan masifa? Mene ne aikinka? Daga ina ka fito? Daga wace al'umma kake?”

9. Sai Yunusa ya ce, “Ni Ba'ibrane ne, ina bin Ubangiji Allah na Sama, wanda ya yi teku da ƙasa.”

10. Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” Sun sani ya gudu ne daga wurin Ubangiji, gama ya riga ya faɗa musu.

11. Hadirin kuwa sai ƙaruwa yake ta yi. Matuƙan jirgin kuwa suka ce masa, “Me za mu yi maka domin tekun ya lafa?”

12. Yunusa ya ce, “Sai ku ɗauke ni ku jefa ni cikin tekun, sa'an nan hadirin zai lafa. Gama na sani saboda ni ne wannan hadiri mai banrazana ya auko muku.”

Karanta cikakken babi Yun 1