Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yow 3:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Zan tattara dukan al'ummai,In kai su kwarin Yehoshafat.A can zan yi musu shari'aA kan dukan abin da suka yi wajama'ata.Sun warwatsa Isra'ilawa a sauranƙasashe,Suka rarraba ƙasata.

3. Sun jefa kuri'a a kan mutanena,Sun sayar da yara, mata da maza,zuwa bautaDon su biya karuwai da ruwaninabi.

4. “Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.

5. Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku.

6. Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa.

7. Yanzu zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, zan yi muku abin da kuka yi musu.

8. Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza 'ya'yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”

9. Ku sanar wa al'ummai da wannan,Su yi shirin yaƙi,Su kira mayaƙa!Su tattaro sojoji, su zo!

10. Su bubbuge allunan garmunansu,Su yi takuba da su.Su ƙera māsu da wuƙaƙen da akeyi wa itatuwa aski.Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumine!”

11. Su gaggauta, su zo su al'ummai dasuke kewaye,Su tattaru a kwarin.“Ya Ubangiji, ka saukar darundunarka mai ƙarfi.”

12. “Sai al'ummai su yi shiri,Su zo kwarin Yehoshafat,Gama a can zan zauna in shara'antaal'umman da suke kewaye,

13. Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi.Su shiga su tattaka,Gama wurin matsewar ruwan inabiya cika.Manyan randuna sun cika sunatumbatsa,Gama muguntarsu da yawa take.”

14. Dubun dubbai suna cikin kwarin daza a yanke shari'a!Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa akwarin yanke shari'a.

15. Rana da wata sun yi duhu,Taurari kuma ba su haskakawa.

Karanta cikakken babi Yow 3