Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yow 2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Fāra ta Zama Musu Alamar Ranar Ubangiji

1. Ku busa ƙaho, ku yi gangami,A cikin Sihiyona, tsattsarkandutsen Allah!Duk mutanen ƙasar za su yi rawarjiki,Domin ranar Ubangiji tana zuwa, tayi kusa.

2. Za ta zama rana ce mai duhudulum,Ranar gizagizai ce baƙi ƙirin.Runduna mai ƙarfi tana tasowa,Kamar ketowar hasken safiya bisatsaunuka.Faufau ba a taɓa ganin irinta ba,Ba kuwa za a sāke ganin irinta ba.

3. Tana cinye shuke-shuke kamar wuta,Ƙasa kamar gonar Adnin take kafinta zo,Amma a bayanta ta zama hamada,Ba abin da ya tsere mata.

4. Kamar doki take,Tana gudu kamar dokin yaƙi.

5. Motsin tsallenta a kan duwatsukamar Motsin karusa ne.Kamar kuma amon wutar da take cintattaka.Kamar runduna mai ƙarfi wadda taja dāgar yaƙi.

6. Da zuwanta mutane sukan firgita,Dukan fuskoki sukan ɓaci.

7. Takan auka kamar mayaƙa,Takan hau garu kamar sojoji,Takan yi tafiya,Kowa ta miƙe sosai inda ta sagaba,Ba ta kaucewa.

8. Ba ta hawan hanyar juna,Kowa tana bin hanyarta.Takan kutsa cikin abokan gāba, ba aiya tsai da ita.

9. Takan ruga cikin birni,Takan hau garu a guje,Takan hau gidaje,Takan shiga ta tagogi kamar ɓarawo.

10. Duniya takan girgiza saboda ita,Sammai sukan yi rawar jiki.Rana da wata sukan duhunta,Taurari kuwa sukan dainahaskakawa.

11. Ubangiji yakan umarci rundunarsa,Rundunarsa mai cika umarninsababba ce, mai ƙarfi,Gama ranar Ubangiji babba ce maibanrazana.Wa zai iya daurewa da ita?

Jinƙan Ubangiji

12. “Koyanzu,” in ji Ubangiji,“Ku juyo wurina da zuciya ɗaya,Da azumi, da kuka, da makoki,

13. Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinkukaɗai ba.”Ku komo wurin Ubangiji Allahnku.Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai,Mai jinkirin fushi ne, mai yawanƙauna,Yakan tsai da hukunci.

14. Wa ya sani ko Ubangiji Allahnmu zaisāke nufinsa,Ya sa mana albarka,Har mu miƙa masa hadaya ta gari data sha?

15. Ku busa ƙaho a Sihiyona,Ku sa a yi azumi,Ku kira muhimmin taro.

16. Ku tattara jama'a wuri ɗaya,Ku tsarkake taron jama'a,Ku tattara dattawa da yara,Har da jarirai masu shan mama.Ku sa ango ya fito daga cikinturakarsa,Amarya kuma ta fito daga cikinɗakinta.

17. Sai firistoci masu hidimar Ubangiji,Su yi kuka a tsakanin shirayi dabagade,Su ce, “Ya Ubangiji, ka cecijama'arka,Kada ka bar gādonka ya zama abinzargiDa abin ba'a a tsakiyar al'ummai.Don kada al'ummai su ce,‘Ina Allahnsu?’ ”

18. Sai Ubangiji ya ji kishin ƙasarsa,Ya kuma ji ƙan mutanensa.

19. Sa'an nan ya ce musu,“Ga shi, zan ba ku hatsi da ruwaninabi, da mai,Za ku ƙoshi.Ba zan sa ku ƙara zama abin zargi gaal'ummai ba.

20. Zan kawar muku da waɗanda sukazo daga arewa,Zan kori waɗansunsu zuwa cikinhamada.Zan kori sahunsu na gaba zuwa cikinTekun Gishiri,Zan kori sahunsu na baya, zuwacikin Bahar Rum.Gawawwakinsu za su yi ɗoyi.Zan yi musu haka saboda dukan abinda suka yi muku.”

21. Kada ki ji tsoro, ya ƙasa,Ki yi farin ciki, ki yi murna,Gama Ubangiji ne ya yi waɗannanmanyan al'amura.

22. Kada ku ji tsoro, ku dabbobinsaura,Gama wuraren kiwo a jeji sun yi koreshar.Itatuwa suna ta yin 'ya'ya,Itacen ɓaure da kurangar inabi sunata yin 'ya'ya sosai.

23. Ya ku mutanen Sihiyona, ku yimurna,Ku yi farin ciki da UbangijiAllahnku,Gama ya ba ku ruwan farkoDomin shaidar gafarar da ya yimuku,Ya kwararo muku da ruwan farko dana ƙarshe da yawa kamar dā.

24. Masussukai za su cika da hatsi,Wuraren matse ruwan inabi za sumalala da ruwan inabi.

25. “Zan mayar muku da abin da kukayi hasararsaA shekarun da fara ta cinyeamfaninku,Wato ɗango da fara mai gaigayewa,da mai cinyewa,Su ne babbar rundunata wadda naaiko muku.

26. Yanzu za ku ci abinci a wadace kuƙoshi,Za ku yabi sunan UbangijiAllahnku,Wanda ya yi muku abubuwa masubanmamaki,Ba kuma za a ƙara kunyatar damutanena ba.

27. Ku mutanen Isra'ila, za ku sani inacikinku,Ni ne kuwa Ubangiji Allahnku, bawani kuma,Ba kuma za a ƙara kunyatar damutanena ba.”

Za a Ba da Ruhun Allah

28. “Bayan wannan zan zubo Ruhuna akan jama'a duka,'Ya'yanku mata da maza za su iyarda saƙona,Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai,Samarinku za su ga wahayi da yawa.

29. A lokacin zan zubo Ruhuna,Har a kan barori mata da maza.

30. “Zan yi faɗakarwa a kan wannanranaA sararin sama da a duniya.Za a ga jini, da wuta, da murtukewarhayaƙi,

31. Rana za ta duhunta,Wata zai zama ja wur kamar jini,Kafin isowar babbar ranan nan maibantsoro ta Ubangiji.