Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yow 1:17-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Itatuwa sun mutu a busasshiyarƙasa,Ba hatsin da za a adana a rumbu,Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.

18. Dabbobi suna nishi!Garkunan shanu sun ruɗeDomin ba su da makiyaya.Garkunan tumaki da awaki kumasuna shan azaba.

19. Ina kuka a gare ka, ya Ubangiji,Domin ciyayi da itatuwa sun bushe,Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.

20. Har ma namomin jeji suna kuka agare ka,Domin rafuffuka sun bushe,Ciyayi kuma sun bushe,Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.

Karanta cikakken babi Yow 1