Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yow 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Maganar Ubangiji zuwa ga Yowel, ɗan Fetuwel.

2. Ku dattawa, ku kasa kunne,Bari kowa da kowa da yake cikinYahuza, ya kasa kunne.Wani abu mai kamar wannan ya taɓafaruwa a lokacinku,Ko a lokacin kakanninku?

3. Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa,'Ya'yanku kuma su faɗa wa'ya'yansu,'Ya'yansu kuma su faɗa wa tsaramai zuwa.

4. Abin da ɗango ya bari fara ta ci,Abin da fara ta bari burduduwa taci.

5. Ku farka, ku yi ta kuka, kubugaggu,Ku yi kuka, ku mashayan ruwaninabi,An lalatar da 'ya'yan inabinDa ake yin sabon ruwan inabi da su.

Karanta cikakken babi Yow 1