Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 8:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da ma a ce kai ɗan'uwana ne, wanda mahaifiyata ta goya,Da in na gamu da kai a titi,Sai in sumbace ka, ba wanda zai kula.

2. Sai in kai ka gidan mahaifiyata,In ba ka gaurayayyen ruwan inabina wanda aka yi da rumman, ka sha.

3. In ta da kai da hannun hagunka,Ka rungume ni da hannun damanka.

4. Ku yi mini alkawari, ku matan Urushalima,Ba za ku shiga tsakaninmu ba.

5. Wace ce take zuwa daga cikin jeji,Kafaɗa da kafaɗa da ƙaunataccenta?A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke,A wurin da aka haife ki,Wurin da mahaifiyarki ta haife ki.

6. Kada ki ƙaunaci kowa sai ni,Kada ki rungume kowa sai ni.Ikon ƙauna kamar na mutuwa ne,Ƙarfin kishin ƙauna kamar na mutuwa ne.Yakan kama kamar wuta,Yakan ci kamar gagarumar wuta.

7. Kome yawan ruwa ba zai iya kashe ta ba.Ba rigyawar da za ta nutsar da ita.Duk wanda ya ce zai iya sayen ƙauna da dukiya,Ba abin da zai same shi sai tashin hankali.

Karanta cikakken babi W. W. 8