Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 7:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Kin ɗaga kanki sama kamar Dutsen Karmel.Kitsattsen gashin kanki kamar shunayya mafi kyau ne,Yakan kama hankalin sarki.

6. Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,Kina sa ni jin daɗi a rai.

7. Kina da kyan gani kamar itacen dabino,Mamanki kamar nonnan dabino.

8. Zan hau itacen dabino in tsinko 'ya'yan.Mamanki kamar nonnan inabi suke a gare ni.Numfashinki kamar ƙanshin gawasa ne.

9. Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne.Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena,Ya gangara leɓunan masu barci.

10. Ni ta ƙaunataccena ce, yana bukatata.

11. Zo saurayina, bari mu tafi waje,Mu kwana a karkara.

Karanta cikakken babi W. W. 7