Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 4:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,Ba wanda zai kushe ki!

8. Amaryata, ki taho daga Dutsen Lebanon,Taho daga Lebanon.Ki taho daga ƙwanƙolin Dutsen Amana,Da Dutsen Senir da Harmon,Inda zakuna da damisoshi suke zaune.

9. Kallon idonki, budurwata, amaryata,Da duwatsun da suke wuyankiSun sace zuciyata.

10. Ƙaunarki abar murna ce, ya budurwata, amaryata!Ƙaunarki ta fi ruwan inabi.Ƙanshinki ya fi kowane irin turare ƙanshi.

11. Zaƙin leɓunanki kamar zuma ne, ya budurwata,A gare ni harshenki madara ne da zuma.Tufafinki suna ƙanshi kamar turaren da yake cikin Dutsen Lebanon.

12. Budurwata, amaryata, ke asirtaccen lambu ce,Lambu mai katanga, asirtacciyar maɓuɓɓuga.

13. Shuke-shuke suna girma sosai.Suna girma kamar gonar itatuwan rumman.Suna ba da 'ya'ya mafi kyauDa kayan shafe-shafe kamar su lalle da nardi.

14. Nardi, da asfaran, da kalamus, da kirfa,Da dukan itatuwan da suke ba da kayan ƙanshi,Da mur, da aloyes, da dukan turare mafi ƙanshi.

15. Maɓuɓɓugai suna ba lambun ruwa, ruwan rafuffuka suna gudu,Ƙoramu suna bulbulo ruwa daga Dutsen Lebanon.

Karanta cikakken babi W. W. 4