Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 4:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kyakkyawa ce ke ƙaunatacciyata.Idonki kamar na kurciya, suna haskakawa daga cikin lulluɓi.Gashinki yana zarya kamar garken awakiDa yake gangarowa daga tuddan Gileyad.

2. Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya,Aka yi mata wanka nan da nan.Ba giɓi, suna nan shar.An jera su tantsai.

3. Leɓunanki ja wur kamar kin shafa jan-baki.Maganarki tana faranta zuciya.Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.

4. Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda yake, kewayayye sumul sumul,Inda aka rataye garkuwoyi dubu na jarumawa.

5. Mamanki kamar bareyi biyu ne,Wato tagwayen barewa, suna kiwo cikin furen bi-rana.

Karanta cikakken babi W. W. 4