Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 1:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Faɗa mini, ƙaunataccena,Ina za ka kai garkenka kiwo?Ina za su huta sa'ad da rana ta take?Ina zan neme ka a cikin garkunan makiyaya?

8. Mafi kyau cikin mata, ashe, ba ki san wurin ba?Tafi, ki bi garken,Ki samar wa awakinki wurin kiwoKusa da alfarwan makiyaya.

9. Ke ƙaunatacciyata, kina ɗauke hankalinaKamar yadda goɗiya take ɗauke hankalin ingarmun karusan Fir'auna.

10. Kitsonki yana da kyau a kumatunki,Ya sauka a wuyanki kamar lu'ulu'ai.

11. Mu kuma za mu ƙera miki sarƙar zinariya,A yi miki ado da azurfa.

12. A sa'ad da sarki yake kan kujerarsa,Yana jin daɗin ƙanshin turarena ƙwarai.

13. Ƙaunataccena yana da ƙanshin murLokacin da yake kwance a ƙirjina.

14. Ƙaunataccena kamar furen jeji yakeWanda yake huda a gonar inabi a En-gedi.

15. Ke kyakkyawa ce ƙwarai, kyakkyawa ce ke, ya ƙaunatacciyata,Idonki suna haskaka da ƙauna.

16. Kai kyakkyawa ne ƙwarai, ya ƙaunataccena, kana da bansha'awa.Koriyar ciyawa ita ce gadonmu.

17. Itatuwan al'ul su ne jigajigan gidanmu,Itatuwan fir su ne rufin gidan.

Karanta cikakken babi W. W. 1