Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 1:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga waƙar Sulemanu mafi daɗi.

2. Leɓunanka sun lulluɓe ni da sumba,Ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.

3. Akwai ƙanshi kuma kewaye da kai,Jin amon sunanka yana tunasar da ni.Ba wata matar da za ta ƙi ƙaunarka.

4. Ka ɗauke ni mana, mu gudu,Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka.Da yake kana nan za mu yi farin ciki,Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki.Ya dace a ƙaunace ka!

5. Rana ta sa na zama akawala kyakkyawa.Matan Urushalima, bisa ga launi, ni ƙasa ƙasa ce,Kamar alfarwar hamada,Kamar labulen fādar Sulemanu.

6. Kada ka raina ni saboda launina,Domin rana ta dafe ni.'Yan'uwana suna fushi da ni,Sun sa ni aiki a gonar inabi.Ba ni da zarafin da zan lura da kaina.

7. Faɗa mini, ƙaunataccena,Ina za ka kai garkenka kiwo?Ina za su huta sa'ad da rana ta take?Ina zan neme ka a cikin garkunan makiyaya?

Karanta cikakken babi W. W. 1