Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 3:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ya ce, “Wace ce?”Sai ta amsa, “Ni ce Rut, baranyarka, sai ka rufe ni da mayafinka, gama kai dangi ne na kusa.”

10. Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya sa miki albarka 'yata, yanzu kin nuna alheri mafi girma fiye da na dā da yake ba ki nemi saurayi, matalauci ko attajiri ba.

11. Yanzu dai, 'yata, kada ki damu, zan yi miki dukan abin da kika roƙa, gama dukan mutanen garin sun sani ke macen kirki ce.

12. Gaskiya ce, ni dangi na kusa ne, amma akwai wanda yake dangi na kusa fiye da ni.

13. Ki dakata nan sai gobe, da safe za mu gani, idan shi zai cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Idan ya cika, to, da kyau, amma idan bai cika ba, na rantse da Allah mai rai, zan cika wajibin dangi na kusa a gare ki. Ki kwanta sai da safe.”

14. Sai ta kwanta a wajen ƙafafunsa har safiya. Sa'an nan ta tashi tun da jijjifi kafin a iya gane fuskar mutum, gama ba ya so a sani mace ta zo masussukar.

15. Bo'aza ya ce mata, “Kawo mayafinki, ki shimfiɗa shi.” Sai ta shimfiɗa mayafin, ya zuba mata sha'ir ya kusa garwa huɗu ya aza mata a kā. Sa'an nan ta koma gari.

16. Lokacin da ta zo wurin surukarta, sai surukarta ta ce mata, “'Yata, ina labari?”Sai ta faɗa mata dukan abin da mutumin ya faɗa mata.

17. Ta kuma ce, “Ga sha'ir da ya ba ni, gama ya ce, ‘Ba za ki koma wurin surukarki hannu wofi ba.’ ”

18. Sai surukarta ta ce, “Ki jira dai, 'yata, har ki ga yadda al'amarin zai zama, gama mutumin ba zai huta ba, sai ya daidaita al'amarin a yau.”

Karanta cikakken babi Rut 3