Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Oba 1:4-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ko da yake kina shawagi can samakamar gaggafa,Gidanki kuma yana can cikin taurari,Daga can zan saukar da ke,” in jiUbangiji

5. “Idan ɓarayi sun shiga gidanki,Idan kuma 'yan fashi sun shigagidanki da dare,Yaya za su washe ki?Za su sace abin da ya ishe su nekaɗai,Idan kuma ɓarayin 'ya'yan inabisun shiga gonar inabinki,Za su bar miki kala kurum.

6. Isuwa, wato Edom, ga taskarka,An washe ta ƙaƙaf!

7. Waɗanda kake amana da su,Za su kore ka daga ƙasarka.Mutanen da suke amana da kai,Za su yaudare ka,Su ci ka da yaƙi.Abokan nan naka da kake ci tare dasu za su kafa maka tarko,Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayonnan nasa?’ ”

8. Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zanhukunta Edom,Zan hallaka masu hikimarka,Zan shafe hikima daga dutsenIsuwa.

9. Jarumawanka za su firgita, yaTeman,Za a kashe kowane mutum dagadutsen Isuwa.

10. “Saboda kama-karyar da ka yi waYakubu ɗan'uwanka,Za a sa ka ka sha kunya,Za a hallaka ka har abada.

11. A ranan nan ka tsaya kawai,A ranar da abokan gāba suka fasaƙofofinsa.Suka kwashe dukiyarsa,Suka jefa kuri'a a kan Urushalima.Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.

12. Ba daidai ba ne ka yi murnaSaboda wahalar da ta samiɗan'uwanka.Ba daidai ba ne ka yi farin cikiSaboda halakar mutanen Yahuza.Ba daidai ba ne ka yi musu dariyaA ranar wahalarsu.

13. Ba daidai ba ne ka shiga ƙofarjama'ataA ranar da suke shan masifa.Ba daidai ba ne ka yi murnaA kan bala'in ɗan'uwanka.Ba daidai ba ne ka washe dukiyarsaA ranar masifarsa.

14. Ba daidai ba ne ka tsaya a mararraba,Don ka kashe waɗanda suke ƙoƙarintserewa.Ba daidai ba ne ka ba da waɗandasuka tsere a hannun maƙiyansuA ranar wahala.”

15. “Ranar da ni Ubangiji zanshara'anta al'ummai duka ta zokusa,Ke, Edom, abin da kika yi,Shi ne za a yi miki.Ayyukanki za su koma a kanki.

16. Kamar yadda kuka sha hukunci akan tsattsarkan dutsena,Haka dukan sauran al'umma za su yita sha.Za su sha, su yi tangaɗi,Su zama kamar ba su taɓa kasancewaba.”

17. “Amma za a sami waɗanda za sutsira daga Dutsen Sihiyona,Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki.Jama'ar Yakubu za ta mallakimallakarta.

18. Jama'ar Yakubu za ta zama kamarwuta,Jama'ar Yusufu kuwa kamarharshen wuta,Jama'ar Isuwa za ta zama kamartattaka.Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zaitsira.Ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Oba 1