Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 7:43-66-69 Littafi Mai Tsarki (HAU)

43. Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba'in da huɗu.

44. Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas.

45. Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.

46-56. Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su neZuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,Keros, da Siyaha, da Fadon,Lebana, da Hagaba, da Shamlai,Hanan, da Giddel, da Gahar,Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,Gazam, da Uzza, da Faseya,Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa,Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,Bazlut, da Mehida, da Harsha,Barkos, da Sisera, da Tema,Neziya, da Hatifa.

57-59. Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su nena Sotai, da Hassoferet, da Feruda,Yawala, da Darkon, da Giddel,Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.

60. Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.

61-62. Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra'ilawa ba, su ɗari shida ne da arba'in da biyu.

63. Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri 'yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa.

64. Waɗannan suka nema a rubuta su tare da waɗanda aka rubuta jerin sunayen asalinsu, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.

65. Sai mai mulki ya faɗa musu kada su ci abinci mafi tsarki, sai an sami firist wanda zai yi tambaya ta wurin Urim da Tummin tukuna.

66-69. Jimillar waɗanda suka komo duka su dubu arba'in da dubu biyu da ɗari uku da sittin ne (42,360)barorinsu mata da maza, waɗanda yawansu ya kai dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337)mawaƙa ɗari biyu da arba'in da biyar mata da mazadawakansu kuma ɗari bakwai da talatin da shida nealfadaransu kuma ɗari biyu da arba'in da biyar neraƙumansu ɗari huɗu da talatin da biyar nejakunansu dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720)

Karanta cikakken babi Neh 7