Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 4:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Da na ga mutane sun damu, sai na tashi na yi magana da shugabanni, da sauran jama'a, na ce, “Kada ku ji tsoro, ku tuna da Ubangiji mai iko, mai banrazana, ku yi yaƙi domin 'yan'uwanku, da 'ya'yanku mata da maza, da matanku, da gidajenku.”

15. Da abokan gābanmu suka ji mun san shirinsu, Ubangiji kuwa ya wargaje shirinsu, sai dukanmu muka koma wurin garun, kowa ya kama aikinsa.

16. Daga wannan rana, sai rabin barorina suka yi ta gini, rabi kuwa suna riƙe da māsu, da garkuwoyi, da bakuna, da sulke. Shugabannin kuwa suka goyi bayan dukan Yahudawa sosai.

17. Masu ginin garun da masu ɗaukan kaya suna yi da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma na riƙe da makami.

18. Kowane magini yana rataye da takobinsa sa'ad da yake gini. Mai busa ƙaho yana kusa da ni.

19. Sai na ce wa manya da shugabanni, da sauran jama'a, “Aikin nan babba ne, mai yawa kuma, ga shikuwa, muna rarrabe a kan garun nesa da juna.

20. Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu.”

21. Haka kuwa muka yi aikin, rabinmu na riƙe da māsu tun daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari.

22. A wannan lokaci kuma na ce wa jama'a, kowane mutum tare da baransa ya kwana a Urushalima domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.

23. Saboda haka ni, da 'yan'uwana, da barorina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa. Kowa yana riƙe da makami.

Karanta cikakken babi Neh 4