Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 13:20-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Sau ɗaya ko sau biyu, 'yan kasuwa da masu sayar da abubuwa iri iri suka kwana a bayan Urushalima.

21. Amma na tsauta musu, na ce, “Me ya sa kuka kwana a bayan garu? Idan kun ƙara yin haka zan kama ku.” Tun daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabar ba.

22. Sai kuma na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu, su yi tsaron ƙofofin don a kiyaye ranar Asabar da tsarki.“Ya Allahna, ka tuna da wannan aiki nawa, ka rayar da ni saboda girman madawwamiyar ƙaunarka.”

23. A waɗannan kwanaki kuma na ga waɗansu Yahudawa waɗanda suka auro mata daga Ashdod, da Ammon, da Mowab.

24. Rabin 'ya'yansu suna magana da harshen Ashdod, ko wani harshe dabam, amma ba su iya yin magana da harshen Yahuza ba.

25. Sai na yi musu faɗa na la'ance su, na bugi waɗansu daga cikinsu, na ciccire gashin kansu, na sa su rantse da Allah, cewa ba za su aurar da 'ya'yansu mata ga 'ya'yan maza na bare ba, ko kuma su auro wa 'ya'yansu maza 'yan matan bare, ko su auro wa kansu.

26. Na faɗa musu cewa, “Ba a kan irin wannan ba ne Sulemanu Sarkin Isra'ila ya yi laifi? A al'ummai, ba sarki kamarsa. Allahnsa ya ƙaunace shi, ya sarautar da shi a Isra'ila, duk da haka baren mata suka sa shi ya yi zunubi.

27. Ba za mu yarda da abin da kuke yi ba, har mu aikata wannan mugunta ta rashin aminci ga Allahnmu, da za mu auro baren mata.”

28. Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yoyada ɗan Eliyashib, babban firist, surukin Sanballat ne, Bahorone, saboda haka sai na kore shi daga wurina.

29. “Ka tuna da su, ya Allahna don sun ƙazantar da aikin firistoci da alkawarin zama firist da Lawiyawa.”

30. Da haka na tsarkake su daga kowane baƙon abu, na sa firistoci da Lawiyawa cikin aiki, kowa ya kama aikinsa.

31. Na kuma shirya yadda za a tara itace domin yin hadaya a kan kari, da kuma lokacin da za a kawo nunan fari.“Ya Allahna, ka tuna da ni, ka yi mini alheri.”

Karanta cikakken babi Neh 13